Nijeriya ta ware ranakun 18 ga watan Nuwamban kowace shekara a matsayin ranar fadakar da jama’a kan cutar noma da ke lalata fuska, inda ake gudanar da tarurrukan wayar da kan mutane dangane da illar cutar da kuma yadda ake maganin ta.
Kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontier MSF, tare da ma’aikatar lafiya ta Nijeriya, sun hada kai wajen shawo kan wannan cuta.
Yanzu haka dai kungiyar agajin ta taimaka wajen yi wa mutane sama da 500 da su ka kamu da cutar aiki daga shekara ta 2015 zuwa yanzu, domin ganin an gyara masu fuskokin su a asibitin da ke Sokoto.
Daya daga cikin wadanda su ka ci gajiyar shirin bayan kamuwa da cutar Mulikat Okonlawo, ta ce daga cikin alamun farko na kamuwa da cutar da ya kamata a maida hankali akwai zazzabi da kuma zafin jiki.
Kwararru kan lafiya sun bayyana rashin samun abinci mai gina jiki da kuma rashin tsafta a matsayin manyan abubuwan da ke haddasa kamuwa da wannan cuta, duba da cewa cutar ta na mamayar jikin dan adam ne a daidai lokacin da karfin garkuwar jikin sa ya yi kasa sosai.