Home Labaru Wata Sabuwa: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Gomman Mutane A Jihar Zamfara

Wata Sabuwa: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Gomman Mutane A Jihar Zamfara

540
0

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Karaye da ke karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara, tare da hallaka mutane da dama baya ga kona gidajen su.

Mazauna kauyen Karaye sun ce ba su taba ganin tashin hankali makamancin wannan ba.

Sun ce ‘yan bindigar sun je ne a kan babura dauke da adduna, da bindigogi tare da yi wa kauyen kawanya, sun kuma kwashe sa’o’i da dama su na cin Karen su babu babbaka, sai dai sun zargi jami’an tsaro cewa ba su kai masu dauki ba.

Daga cikin wadanda aka kashe akwai mata da kananan yara da tsofaffi.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara DSP Muhammad Shehu ya shiada wa manema labarai cewa, da alama harin na ramuwar gayya ne, sakamakon wani artabu da aka yi kwanakin baya tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan sintiri a yankin. DSP Shehu, ya ce mutane 14 ne su ka mutu, yayin da wasu 10 su ka samu rauni, sannan kafin zuwan jami’an tsaro maharan sun tsere.