Home Labaru Zaben Kogi Yahaya Bello Ya Yi Nasara Da Kuri’u 406,222

Zaben Kogi Yahaya Bello Ya Yi Nasara Da Kuri’u 406,222

522
0
Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi Kuma Dan Takarar Jam’iyyar APC
Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi Kuma Dan Takarar Jam’iyyar APC

Gwamnan jihar Kogi kuma dan takarar jam’iyyar APC Yahaya Bello ya yi nasara a zaben da aka gudanar a jihar.

Baturen zaben ya sanar da cewa, Yahaya Bello ya samu kuri’u dubu 406 da 222, yayin da Musa Wada na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u dubu 189 da 704, ‘yar takarar jam’iyyar SDP Natasha Akpoti kuma ta samu kuri’u dubu 9 da 482.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba ne aka gudanar da zaben gwamna da na dan majalisar dattawa da ke wakiltar mazabar Kogi ta Yamma a jihar Kogi.

Sai dai Kungiyoyin sa-ido a kan zaben sun yi watsi da sakamakon da aka tattara na zaben gwamna da sanatan, inda su ka ce an tafka kura-kurai.

Leave a Reply