Home Labarai Kawar Da Ta’addanci: Sojoji Sun Fatattaki Lakurawa Daga Najeriya

Kawar Da Ta’addanci: Sojoji Sun Fatattaki Lakurawa Daga Najeriya

12
0
Sen. Adamu Aliero
Sen. Adamu Aliero

Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Adamu Aliero, ya ce sojojin Najeriya sun samu nasarar fatattakar ƴan Lakurawa, inda suka tsallaka zuwa Nijar.

A wata sanarwa da ya fitar, Aliero ya ce an samu nasarar ne bayan ɗaukar matakin da ministan tsaro Abubakar Bagudu da babban hafsan tsaro da sauran masu ruwa da tsaki suka ɗauka.

Aliero ya ce, sun faɗa wa ministan cewa idan aka yi sakaci da ƴanta’addan Lakurawa, za a iya maimaita abin da ya faru a arewa maso gabas da arewa maso yamma.

Yaƙi ne da za a iya gamawa a kwana biyar, amma idan aka yi sakaci, lamarin zai ƙazance saboda yankin arewa maso yamma ya fi yawan mutane kuma ya fi arziki da ma girman ƙasar noma da kiwo.

Ya ce Lakurawa sun kashe mutane da dama a jihar Kebbi,

lamarin da ya sa Sanata Aliero da sauran ƴan majalisar jihar suka kai ziyara a ƙananan hukumomin Argungu da Augie domin gane wa idonsu irin ɓarnar da suke yi.

Leave a Reply