Home Labaru Karin Haraji: Buhari Ya Ce Gwamnati Ba Ta Yi Hakan Ba Ne...

Karin Haraji: Buhari Ya Ce Gwamnati Ba Ta Yi Hakan Ba Ne Don Jefa Al’umma Cikin Kunci

597
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce karin harajin kayayyaki daga kashi 5 zuwa sama da kashi 7 da gwamnatin tarayya ta ke kokarin aiwatarwa, hakan ba ya na nufin jefa ‘yan Nijeriya cikin kuncin rayuwa ba ne.

Karanta Wannan: Taron Ecowas: Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Burkina Faso Ranar Asabar

Buhari, ya bayyana haka ne lokacin da ya tarbi tawagar shugabannin gamayyar kungiyoyin kwadago ta Nijeriay TUC a fadar sa da ke Abuja.

Shugaban kasa Buhari ya kara da cewa, gwamnatin sa za ta ci-gaba da lalubo hanyoyin saukakawa al’umma kuncin rayuwa musamman ta hanyar aiwatar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata.