Home Labaru Fasa-Kwauri: Babu Ranar Bude Iyakokin Nijeriya – Hamid Ali

Fasa-Kwauri: Babu Ranar Bude Iyakokin Nijeriya – Hamid Ali

1109
0
Shugaban hukumar yaki da fasa-kwauri ta Nijeriya Kanar Hameed Ali
Shugaban hukumar yaki da fasa-kwauri ta Nijeriya Kanar Hameed Ali

Shugaban hukumar yaki da fasa-kwauri ta Nijeriya Kanar Hameed Ali mai ritaya, ya ce za a cigaba da garkame iyakokin Nijeriya har sai kasashen da ke da iyaka da ita sun aminta da dokokin gwamnatin Nijeriya.

Karanta Wannan: Fasakwauri: Mai Yiwuwa Nijeriya Ta Dage Haramcin Shigo Da Motoci

Kanar Hameed Ali ya sanar da haka ne, yayin da ya kai ziyara iyakar Nijeria da jamhuriyar Nijar da ke Maigatari a ranar Larabar da ta gabata, inda ya ce Nijeriya ba za ta kalmashe kafa ta na kallon makwaftan ta na jibgo abubuwan da za su cutar da tattalin arzikin ta ba.

Hameed Ali ya bayyana wa manema labarai cewa, kasashen da ke makwaftaka da Nijeriya, su na taimakawa wajen shigo da ababen da Nijeriya ta haramta, wadanda za su iya kawo zagon kasa ga ci-gaban kasa.

Ya ce duk da wannan mataki, kofa a bude ta ke domin tattaunawa a kan yarjejeniyoyin da za su mutunta dokokin tattalin arzikin Nijeriya.