Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce karin harajin kayayyaki daga kashi 5 zuwa sama da kashi 7 da gwamnatin tarayya ta ke kokarin aiwatarwa, hakan ba ya na nufin jefa ‘yan Nijeriya cikin kuncin rayuwa ba ne.
Karanta Wannan: Taron Ecowas: Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Burkina Faso Ranar Asabar
Buhari, ya bayyana haka ne lokacin da ya tarbi tawagar shugabannin gamayyar kungiyoyin kwadago ta Nijeriay TUC a fadar sa da ke Abuja.
Shugaban
kasa Buhari ya kara da cewa, gwamnatin sa za ta ci-gaba da lalubo hanyoyin saukakawa
al’umma kuncin rayuwa musamman ta hanyar aiwatar da sabon mafi karancin albashin
ma’aikata.