Home Labarai Iran Da Isra’Ila: Gwamnatin Najeriya Ta Bukaci A Kai Zuciya Nesa

Iran Da Isra’Ila: Gwamnatin Najeriya Ta Bukaci A Kai Zuciya Nesa

24
0
Nigeria Federal Ministry of Foreign Affairs have installed SECUSCAN machines
Nigeria Federal Ministry of Foreign Affairs have installed SECUSCAN machines

Gwamnatin Najeriya ta bi sawun sauran kasashen duniya wajen yin kiran a kai zuciya nesa kan barazanar Iran da Isra’ila.

Ta bukaci a ci gaba da tattaunawar diflomasiyya don ganin an kwantar da hankula da kuma kaucewa yaduwar rikici a yankin gabas ta tsakiya.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta fitar a ranar Lahadi, ta yi kira ga kasashen su duba batun warware rikicin cikin lumana, ta ce akwai bukatar samar da zaman lafiya da kuma tsaro a duniya baki-daya.

Hakan na zuwa ne dai bayan da Iran ta kaddamar da hari kan Isra’ila a daren Asabar, inda ta ce harin nata a matsayin ramuwa ne na kisan wasu kwamandojin ta da Isra’ila ta yi a wani hari da ta kai karamin ofishin jakadancin ƙasar a Siriya, ranar 1 ga watan Afrilu, 2024.

Sai dai harin ya bar baya da kura, inda manyan kasashen duniya suka nuna rashin jin dadin su game da matakin na Iran

Leave a Reply