Home Labarai Kano: Gwamna Abba Yusuf Ya Kafa Harsashin Ginin Gadar Saman Da Zata...

Kano: Gwamna Abba Yusuf Ya Kafa Harsashin Ginin Gadar Saman Da Zata Ci Naira Bilyan 15

16
0
Abba Kabir Yusuf Governor Kano State (1)
Abba Kabir Yusuf Governor Kano State (1)

A kokarinsa na maida birnin Kano zuwa katafariyar alkarya, tare da rage mata cunkoson ababen hawa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora harsashin ginin gadar sama mai hawa 3 da zata lakume Naira biliyan 15 a Kofar Dan Agundi.

A ziyarar da yakai wurin da za’a gina gadar, gwamnan bisa rakiyar mukarrabansa, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na sauya taswirar birnin Kano.

Ya kuma jaddada mahimmancin inganta zirga-zirgar ababen hawa a kokarin daga likkafar Kano zuwa katafaren birnin.

Kwangilar aikin, wacce aka baiwa kamfanin gine-gine na “CCG Nigeria Limited” a watan Disambar daya gabata, nada wa’adin kammalawa na watanni 18.

A cewar gwamnan, sun kirkiri hanyoyin kewaye, kuma suna sa ran masu ababen hawa su yi biyayya ga ka’idojin kiyaye afkuwar hadura tare da kyale aikin gadar ya gudana cikin lumana.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, ya fitar tace, samarda ababen more rayuwa da inganta bangaren ilmi, sune bangarorin da gwamnatin Kano mai ci tafi maida hankalinta akai.

Leave a Reply