Home Labarai Tsaro: Zaratan Sojojin Nijar Sun Kama Jagoran Yan Bindigar Najeriya

Tsaro: Zaratan Sojojin Nijar Sun Kama Jagoran Yan Bindigar Najeriya

164
0
91553433 b61bcb02 bb07 4adf 9586 9bbf7da1099c
91553433 b61bcb02 bb07 4adf 9586 9bbf7da1099c

Dakarun sojin Jamhuriyar Nijar sun kama wani jagoran ’yan bindigar Najeriya, Kachallah Mai Daji a kusa da iyakar garin Illela da ke kasar.

Masanin harkar tsaro kuma mai sharihi kan yaki da tayar da kayar baya a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce sojojin Nijar sun kama dan bindigar ne a lokacin da yake kokarin sace dabbobi ya tsallaka iyakar Najeriya da Nijar da su.

Ya ce “Sojojin Nijar sun damke shi yana kokarin satar dabbobi a kan iyakar Najeriya da Nijar.

Zagazola ya bayyana Kachallah Mai Daji a matsayin daya daga cikin hatsabiban yan bindiga da suka shafe shekaru suna addabar yankin Arewacin Najeriya.

A cewarsa, “dan ta’addan ya shafe kusan shekara 10 yana kashe mutane da kona kauyuka da sace jama’a da ma kakaba musu haraji a kauyukansu.”

Kachalla Mai Daji dai ya fi addabar kauykan yankin Illela da suka hada da Tozai, Sabon Garin Darna, Darna Tsolawo, Tudun Gudali, Basanta, Ɗan Kadu, Takalmawa, Gidan Hamma, Ambarura, Gidan Bulutu da sauran makwabtansu.

Leave a Reply