Home Labarai Ziyara Amurka: Shattima Ya Dakatar Da Tafiyarsa

Ziyara Amurka: Shattima Ya Dakatar Da Tafiyarsa

108
0
375746399 866617948160534 8172627323694893843 n (1)
375746399 866617948160534 8172627323694893843 n (1)

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya soke shirinsa na zuwa kasar Amurka domin halartar taron koli kan kasuwanci tsakanin Amurka da Afirka na shekarar 2024 a birnin Dallas na jihar Texas.

Babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Stanley Nkwocha ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya kara da cewa, yanzu ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ne zai wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a taron koli da za a yi a Amurka.

Nkwocha,  ya ce, Kashim Shettima wanda tun farko aka shirya tafiyarsa don wakiltar shugaba Tinubu, an soke tafiyar ne “bayan gano wata matsala da jirginsa ya samu, lamarin da ya tilasta soke tafiyar bisa shawarar masu kula da jirgin.”

Ya kuma kara da cewa, yanzu mataimakin shugaban kasa zai cigaba da gudanar da wasu ayyuka na kasa

Leave a Reply