Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC tare da ta gamayyar kungiyoyin kwadagon TUC, sun nemi gwamnati ta biya Naira dubu 615 ga ko wane ma’aikaci a matsayin mafi karancin albashi.
Kungiyoyin sun tabbatar da cewa sun aike wa kwamitin da mataimakin Shugaban kasa ya nada domin duba yadda za a inganta albashin ma’aikata ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ba bukatar ta su.
Kwamred Nasir Kabir, shugaban tsare-tsare na kungiyar kwadago ta kasa, ya ce mafi karancin albashin (₦615,000) shi ne abin da suka amince da shi, kuma a kan sa za su tsaya, babu gudu babu ja da baya.
Nasir ya ce inda a ra’ayin sa ne, abin da ya kamata a biya ko wanne ma’aikaci ya zama akalla Naira miliyan daya duk wata.
Amma wata ma’aikaciya, ta ce wannan ba abu ne mai yiwuwa ba, domin ko albashin dubu sha takwas da gwamnatin baya ta ce a biya ma’aikata har yanzu wasu jihohi ba su biya ba, balle kuma karin dubu talatin da gwamnatin baya ta yin ta ce in an ce a daga zuwa dubu dari shida har da goma sha biyar babu wanda zai iya biya.














































