Gwamnatin Najeriya ta bi sawun sauran kasashen duniya wajen yin kiran a kai zuciya nesa kan barazanar Iran da Isra’ila.
Ta bukaci a ci gaba da tattaunawar diflomasiyya don ganin an kwantar da hankula da kuma kaucewa yaduwar rikici a yankin gabas ta tsakiya.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta fitar a ranar Lahadi, ta yi kira ga kasashen su duba batun warware rikicin cikin lumana, ta ce akwai bukatar samar da zaman lafiya da kuma tsaro a duniya baki-daya.
Hakan na zuwa ne dai bayan da Iran ta kaddamar da hari kan Isra’ila a daren Asabar, inda ta ce harin nata a matsayin ramuwa ne na kisan wasu kwamandojin ta da Isra’ila ta yi a wani hari da ta kai karamin ofishin jakadancin ƙasar a Siriya, ranar 1 ga watan Afrilu, 2024.
Sai dai harin ya bar baya da kura, inda manyan kasashen duniya suka nuna rashin jin dadin su game da matakin na Iran