Home Labaru Kiwon Lafiya Kiwon Lafiya: Ma’aikatan Jinya Sun Koka Kan Rashin Albashin Watanni 8 A Kaduna.

Kiwon Lafiya: Ma’aikatan Jinya Sun Koka Kan Rashin Albashin Watanni 8 A Kaduna.

14
0
Doctors 350x250
Doctors 350x250

Sabbin ma’aikatan jinya da ungozoma da aka ɗauka aiki a Jihar
Kaduna sun yi kira ga Gwamna Uba Sani da ya sa baki a kan
rashin biyan albashinsu na watanni takwas.


Sama da ma’aikatan lafiya 200 gwamnatin jihar ta ɗauka a watan Yunin 2023 a kan matakin albashi na 7 kuma aka tura su
zuwa manyan asibitocin jihar. Rahotanni na cewa ma’aikatan jinyar sun yi aiki na tsawon watanni ba tare da an biya su albashi ba. Sai dai a kwanan baya an biya su albashin watan Fabarairu da Maris da Afrilu yayin da albashin sauran watanni takwas ɗin
suka maƙale.


Wasu daga cikin ma’aikatan jinyar da abin ya shafa sun yi ikirarin cewa an cire masu wasu kuɗi a cikin albashinsu na Fabarairu da Maris da Afrilu, saɓanin adadin da aka rubuta a takardun ɗaukar aikinsu ba tare da wani bayani daga ma’aikatar ba.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan jinyar wacce ta bayyana sunanta da Ummul Tani saboda tsoron kada a yi mata barazana, ta ce, “Ba a biya su bashin albashin watanni takwas da muka yi aiki ba.

Leave a Reply