Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasar su fara cirar kaso 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da aka tura ta intanet a matsayin harajin tsaron kudade ta kafar.
Sanarawar da daraktan kula da tsarin biyan kuɗi Chibuzor Efobi da kuma Daraktan tsare-tsaren na kuɗi Haruna Mustafa suka sa wa hannu ta ce bankuna za su fara zarar wannan kuɗi nan da makonni biyu.
An gabatar da wannan daftarin ga bankunan kasuwanci da kamfanoni masu hada-hadar biyan kuɗi da dangoginsu.
Sanarwa ta bayyana cewa an cimma wannan matsaya ce bayan la’akari da bukatar tabbatar da kudirin dokar yaƙi da satar kuɗi ta intanet ta shekarar 2015.