Home Labarai Bukatar Tinubu: Ana Ci Gaba Da Cece Kuce Kan Karbo Bashin Dala...

Bukatar Tinubu: Ana Ci Gaba Da Cece Kuce Kan Karbo Bashin Dala Biliyan Biyu

26
0
Bola Tinubu
Bola Tinubu

Ana ci gaba da cecekuce kan bukatar da shugaban kasa Bola Tinubu, ya mika wa majalisun dokoki su amince ya karbo wani sabon bashi na dala biliyan biyu da miliyan dari biyu, wato kusan naira tiriliyan biyu daga waje.

Masu sukar lamarin dai suna ganin ƙaruwar bashin da Najeriya ke ciwowa daga waje wata babbar barazana ce ga gudanar da tattalin arziki yadda ya kamata.

Akwai kuma damuwar da wasu ke ta bayyanawa game da yadda kasafin kudin badi shi ma zai dogara matuka kan bashi.

Tun da bukatar karbo sabon bashin karasa aiwatar da kasafin kudin Najeriyar na bana ta taso dai, ake ta bayyana damuwa kan lamarin.

Kodayake Dokta Murtala AbdulLahi Ƙwara, malami a sashen nazarin tattalin arziki na jami’ar Umaru Musa Ƴar-Adua da ke Katsina, yana ganin har yanzu yawan irin wannan bashi da kasa ke ciwowa daga waje, bai kai ga munana ba.

Leave a Reply