Home Labaru Tashin-Tashina: Farfesa Yemi Osinbajo Ya Zargi Manyan ‘Yan Siyasar Nijeriya

Tashin-Tashina: Farfesa Yemi Osinbajo Ya Zargi Manyan ‘Yan Siyasar Nijeriya

341
0

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya koka da yadda wasu daga cikin ‘yan siyasar Nijeriya ke amfani da rikicin addini da kabilanci domin cimma muradun kan su.

Osinbajo, ya ce manyan ‘yan siyasa ne su ka janyo aka kasa samun zaman lafiya, domin su ke cin gajiyar bakar kiyayyar da ke yawo a zukatun jama’a.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, o ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen bikin taya tsohon gwamnan jihar Ogun Olusegun Osoba murnar cika shekaru 80 a Duniya

Farfesa Osinbajo ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen bikin taya tsohon gwamnan jihar Ogun Olusegun Osoba murnar cika shekaru 80 a Duniya, inda ya ce daya daga cikin rikicin da ‘yan siyasa su ka jefa Nijeriya shi ne, haddasa rashin yarda da jituwa a tsakanin mutane.

Mataimakin shugaban kasar ya ce, ana cin moriyar sabanin addini da kabilancin da aka samu, wanda a cewar sa hakan ba karamin hadari ba ne, don haka ya nemi a yi gaugawar magance wannan gagarumar matsala.

Leave a Reply