Home Labaru Nadin Ministoci: Buhari Zai Gabatar Da Sunayen Su A Cikin Makon Nan...

Nadin Ministoci: Buhari Zai Gabatar Da Sunayen Su A Cikin Makon Nan – Ahmed Lawan

444
0

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce kafin wannan makon ya shude shugaba Muhammadu Buhari zai aika da jerin sunayen ministocin da ya ke son nadawa.

Sanatan ya bayyana haka ne, yayin da ya ke amsa tambayoyi game da jawabin Sanata Albert Bassey Akpan na jam’iyyar PDP, wanda ya nuna damuwa a kan jinkirin da fadar shugaban kasa ke yi na aika sunayen sabbin ministocin.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan

Sanata Albert Bassey dai cewa ya yi, babu yadda za a yi  shugaba Buhari ya ki aikawa da sunayen, yayin da ake saura makonni biyu ‘yan majalisar su tafi hutun watanni biyu.

Sai dai Sanata Lawan cewa ya yi, fadar shugaban kasa na iyakar kokarin ta, wajen tabbatar da cewa majalisar dattawa ta samu jerin sunayen ministocin kafin wannan makon ya shude.

Leave a Reply