Home Labarai Rashin Shaida: Kotu A Barno Ta Bada Umurnin Sakin Mutum 313 Da...

Rashin Shaida: Kotu A Barno Ta Bada Umurnin Sakin Mutum 313 Da Ake Zargi Da Ta’Addanci

37
0

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Borno ta bayar da umarnin sakin mutane akalla 313 da ake zargin ƴan ta’adda ne da sojoji suka kama.

Kotu ta bayar da umarnin a sake su ne saboda rashin shaidar da za ta sa a yi musu hukunci.

Hakan na zuwa ne yayin da shelkwatar tsaron Najeriya ta ce, sojojin sun kashe ƴan ta’adda 121, tare da kama 253 da kuma kubutar da mutum 244 da aka yi garkuwa da su a wasu samame daban-daban da suka kai a cikin mako guda.

Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar tsaro, Manjo Janar Buba Edward ne ya bayyana haka a yayin taron manema labarai kan ayyukan soji a fadin kasa yau Alhamis a nan Abuja.

Janar Buba ya ce za su bi umurnin kutun wajen mika mutanen ga gwamnatin jihar Barno.

Leave a Reply