Home Labarai Kisan Soji 17: Rundunar Sojin Najeriya Na Zargin Sarakunan Delta Da Hannun

Kisan Soji 17: Rundunar Sojin Najeriya Na Zargin Sarakunan Delta Da Hannun

152
0

Babban hafsan tsaro na Najeriya, janar Christopher Musa, ya ce sarakunan gargajiyar yankin Okuama da makwabta da ke jihar Delta, na da hannu a kisan da aka yiwa sojoji 17 a jihar.

A ranar 14 ga watan Maris ne, wasu matasa ‘yan ta’adda suka kaiwa dakarun bataliya ta 181 harin kwanton bauna, abin da ya haifar da mutuwar sojoji 17 ciki har da masu mukamin Manjo guda biyu da kuma mai mukamin Kyaftin guda daya.

A cewar sanarwar da rundunar sojin ta fitar an kaiwa sojojin hari ne lokacin da suke kokarin kwantar da tashin hankalin da ya kunno kai tsakanin kabilar Okuama da kuma Okoloba da ke kudancin Najeriya.

Hakan ta sanya rundunar ta ayyana neman wasu sarakuna takwas ruwa a jallo, sakamakon mutuwar manyan sojojin.

Basaraken masarautar Ewu, da ke yankin karamar hukumar Ughelli a jihar ta Delta, Clement Ikolo wanda ya kasance cikin wadanda shalkwatar rundunar ke nema ruwa a jallo, yanzu haka yana tsare a hannun jami’an tsaro a nan Abuja.

Sai dai sarakunan gargajiyar sun ce basu da hannu a rikicin yankunan da ya kunno wanda hakan ya yi sanadin mutuwar wadannan sojoji 17.

Leave a Reply