Home Labarai TSaikon naɗin jakadun najeriya zuwa ketare: masana diflomasiyya sun nuna damuwa.

TSaikon naɗin jakadun najeriya zuwa ketare: masana diflomasiyya sun nuna damuwa.

49
0

Wasu ‘yan Najeriya sun soma nuna damuwa kan dogon lokacin da gwamnatin ta dauka, ba tare da tura jakadunta wasu kasashen ketare ba.

Masu nuna damuwa na baya-bayan nan, su ne masana diflomasiya, inda suka ce bai kamata kasa kamar Najeriya ta yi jinkiri irin haka ba.

To sai dai masana difomasiya kamar Ambasada Sulaiman Dahiru tsohon jakadan Najeriya a Sudan, ya ce rashin tura wakilan ya nuna cewa gwamnatin ba ta dauki harkar alakar ta da sauran kasashen wajen da muhimanci ba.

Ya ce gwamnati ta yi kuskure, bai kamata ta yi wa jakadun ta da ke kasashen waje kiranyen dawowa gida ba, alhalin ba ta shirya wadanda za su maye gurbin su ba.

Ya ci gaba da cewa a tsari bai kamata Jakada ya bar kasa har na sama da mako biyu ba tare da an tura wanda zai maye gurbin sa ba, domin wannan zai sanya kasashen su yi tunanin ba a daukji mu’amala da su da muhimmanci ba.

Tun watan 9 na bara ne dai aka yi wa Jakadun Najeriya kiranye, hakan na nufin duk abin da Najeriya ta ke son bibiya ba za ta yi ba saboda ba ta da wakili.

Leave a Reply