Home Home Matan Najeriya Fiye Da 25,000 Sun Maƙale A Mali – Naptip

Matan Najeriya Fiye Da 25,000 Sun Maƙale A Mali – Naptip

37
0

Hukumar Yaƙi da Safarar Bil-Adama ta Nijeriya NAPTIP, ta ce aƙalla mata da ‘yan mata ‘yan Nijeriya sama da dubu 25 da aka yi safarar su ne su ka makale a kasar Mali.

Kwamandan hukumar mai kula da shiyyar Benin Mista Nduka Nwanwenne ya bayyana haka, yayin wani taron bita da aka shirya wa ƙwararru a kan harkokin yada labarai a Legas.

Babbar daraktar hukumar Fatima Waziri-Azi, ta ce maƙasudin taron bitar shi ne janyo hankalin ƙwararrun kafafen yada labarai a kan mummunar ɗabi’ar safarar mutane domin ƙara wayar da kan jama’a a kan illolin ta.

Mista Nduka, ya ce binciken da hukumar ta gudanar ya gano cewa, ana yaudarar mafi yawa daga cikin matan ne da kuɗi wajen yin safarar su, domin a cewar sa, binciken su ya gano cewa mazan Mali sun fi kashe wa mata kudi idan aka kwatanta da na Nijeriya.

Kwamandan ya kara da cewa, hukumar ta kama mutane dubu 9 da 102 da ake zargi da safarar mutane, tare da kuɓutar da wasu dubu 20 da 660 tsakanin shekara ta 2004 zuwa 2023.

Leave a Reply