Jakadan ƙungiyar ƙasashen ECOWAS na musamman da ke shiga tsakani a kan rikice-rikicen da ake yi a Mali kuma tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, ya yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu bayani game da abubuwan da ke faruwa a Mali da sauran ƙasashen yammacin Afirka.
Goodluck Jonathan, ya ce ya je fadar shugaban ƙasa ne domin miƙa wa Tinubu sakamakon tattaunawar da ya yi da sauran ‘yan ƙungiyar Afrika ta yamma da ya ke jagoranta.
A matsayin sa na wakilin musamman a ƙungiyar ECOWAS, Jonathan ya na jagorantar tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki a ƙasar Mali, ciki kuwa har da shugaban ƙasa Ibrahim Boubacar Keita da ƙungiyoyin farar hula da na addinai domin warware rikicin zamantakewa da siyasa a ƙasar.
Goodluck Jonathan, ya ce a matsayin shi na mai shiga tsakani na ƙungiyar ECOWAS, akwai batutuwan da su ka shafi nahiyar da kuma yankin da ya ke tattaunawa da shugabanni daban-daban.














































