Home Home Tinubu Ya Umarci Kai Agaji Ga ‘Yan Bikin Da Jirgin Ruwa Ya...

Tinubu Ya Umarci Kai Agaji Ga ‘Yan Bikin Da Jirgin Ruwa Ya Kife Da Su A Kwara

39
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarnin a kai kayan agaji da taimakon da ya wajaba nan take ga mutanen da su ka kuɓuta da dangi da iyalan waɗanda su ka mutu a hatsarin jirgin ruwa a jihar Kwara.

Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na shugaban kasa Abiodun Oladunjoye ya fitar, ta ambato shugaba Tinubu na cewa ya yi takaicin hatsarin jirgin ruwa da ya kashe mutane 150 a jihar Kwara.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci gwamnatin jihar Kwara da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da lamarin ya shafa, su yi aiki tare domin gano musabbabin aukuwar hatsarin jirgin ruwan.

Mutanen da hatsarin ya ritsa da su dai ‘yan biki ne da ke kan hanyar komawa gida daga ƙauyen Egbu na ƙaramar hukumar Patigi.

Shugaba Tinubu ya kuma yi alƙawarin cewa, gwamnatin shi za ta yi nazari a kan matsalolin sufurin ruwa a Nijeriya domin tabbatar da ganin ana aiki sau da ƙafa da matakan kare rayuka da ƙa’idojin aiki.

Leave a Reply