Home Labaru Hukunci: Sojojin Najeriya 14 Za Su Amsa Tuhuma Kan Garkuwa Da Mutane

Hukunci: Sojojin Najeriya 14 Za Su Amsa Tuhuma Kan Garkuwa Da Mutane

378
0

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta gurfanar da jami’an ta guda 14 da ake tuhuma da hannu wajen garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kisan kai da kuma tserewa daga bakin aiki.
Kwamandan runduna ta 6 da ke Fatakwal, Janar Jamil Sarham ya ce wadanda ake zargin sun hada manyan jami’ai da kuma kanana.
Janar Sarham, ya ce laifuffukan da ake tuhumar jami’an na karkashin dokar soji ta 20, kuma saida aka kammala binciken kowanne jami’I kafin gurfanar da su a gaban kotun sojin.
Alkalan kotun guda 7 na karkashin jagorancin Janar Bassey Etuk.

Leave a Reply