Home Labaru Zamfara: An Sake Kashe Mutane Da Dama A Hari

Zamfara: An Sake Kashe Mutane Da Dama A Hari

266
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa an kashe mutum 34 a wani hari da ‘yan fashi suka kai kan kauyen Tungar Kahau a karamar hukumar Shinkafi.
Sai dai wasu mazaunan yankin Shinkafi sun ce mutanen da aka kashe sun kai 42, inda a ranar da aka kai harin aka samu gawawwakin mutum 40, kafin washe gari kuma a gano karin gawa biyu.
Wannan shi ne na baya-bayan nan cikin hare-haren ‘yan fashi wadanda suka addabi jihar Zamfara, da ma karin wasu jihohi da ke makwabtaka da ita.
Bayanai sun ce tuni mutanen Tungar Kahau suka tsere zuwa manyan garuruwa dake ciki da wajen jihar Zamfara bayan harin.
Wani mazaunin kauyen ya ce mutanen kauyen gaba daya sun watse, saboda kowa na dar-dar kada dare ya yi masa a kauye.
Haka zalika wani da ya tsira daga harin ya shaida wa BBC cewa da yamma ne kwatsam maharan suka auka musu da harbin kan mai-uwa-da-wabi.
Mai magana da yawun rundunar, Muhammed Shehu ya ce tuni aka tura karin jami’an tsaro da suka je yankin domin farautar maharan a cikin daji.

Leave a Reply