Home Labaru Almundahana: Kwamitin Bincike Zai Tuhumi Tsohon Gwamnan Jihar Gombe Dankwambo

Almundahana: Kwamitin Bincike Zai Tuhumi Tsohon Gwamnan Jihar Gombe Dankwambo

322
0

Tsohon gwamnan jihar Gombe Dankwambo na karkashin bincike kan zargin rashawa da kuma siyar da kayayyakin jihar ba bisa ka’ida ba.
Kwamitin dawo da kayayyakin gwamnatin jihar Gombe a karkashin jagorancin kyaftin Peter Bilal mai ritayane ya gayyaci Dankwambo domin ya amsa tambayoyi.
Bilal, ya ce kwamitin zai dauki matakin doka idan Dankwambo da hadimansa da aka gayyata suka ki zuwa domin amsa tambaya.
Kwamitin wanda Kyaftin Peter Bilal mai ritaya ke jagoranta, ya ce anyi gayyatar ne domin tsohuwar gwamnati ta bayar da bayanai kan kayayyakin jihar da ta siyar ba bisa ka’ida ba.
Shugabn kwamitin ya ce kwamitin zai dauki matakin doka domin dawo da arzikin jihar idan suka ki gurfana a gabanta.

Leave a Reply