Home Labaru Harin Borno: ISWA Ta Dauki Nauyin Kisan Kwamandan Sojojin Nijeriya

Harin Borno: ISWA Ta Dauki Nauyin Kisan Kwamandan Sojojin Nijeriya

516
0

Kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWA sun bayyana cewa, su ne su ka kai wa bataliya ta 158 da ke Jihar Borno hari, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji ciki har da kwamandan bataliyar mai mukamin Laftanar Kanar.

Idan dai ba a manta ba, a wani harin kare-dangi da kungiyar Boko Haram suka kai wa bataliyar sojoji ta 158 da ke Borno, ya yi sanadiyyar mutuwar wani kwamandan Sojojin Nijeriya.

Bayan sanar wa rundunar sojin Nijeriya haka ne, nan take ta tura dakaru domin su kai wa sansanin dauki.

Rahotanni sun nuna cewa, maharan sun arce zuwa kauyen Fuchimiram, wanda akalla kilomita 6 ne daga Kareta a karamar hukumar Mobba.

Leave a Reply