Wasu matan jam’iyyar APC sun taya shugaba Muhammadu Buhari murnar gudanar da bikin ranar dimokradiyya ta Nijeriya ranar bikin farar hula a Najeriya inda a ka yi bikin murnar zarcewarsa a kan mulki.
Haka kuma, matan sun yi wa shugaba Buhari addu’o’in samun karin lafiya domin ya jagoranci Nijeriya ba tare da samun matsaloli ba a karkashin jagorancin Adedoyin Eshanumi.
Misis Eshanumi, ta jagoranci sauran takwarorin ta mata da su ka yi takara a karkashin jam’iyyar APC a zaben shekara ta 2019, domin yi wa shugaba Buhari addu’ar samun iko da basira da lafiyar mulkin Nijeriya.
Matan, sun kuma nemi shugaba Muhammadu Buhari ya rika damawa da su a sha’anin mulki cikin shekaru hudu masu zuwa, domin sun nuna wa jam’iyyar APC goyon baya a shekara ta 2019.
Eshanumi, ta ce a cikin mata 360 da su ka nemi takara a zaben da ya gabata, kasa da kashi daya ne kadai su ka yi nasara, don haka ta nemi shugaba Buharir ya tafi da su a wa’adin mulkin san a biyu.
You must log in to post a comment.