Home Labaru Rikicin Sudan: Omar Al Bashir Zai Gurfana A Gaban Kotu

Rikicin Sudan: Omar Al Bashir Zai Gurfana A Gaban Kotu

332
0

Babban mai shigar da kara a kasar Sudan Al-Waleed Sayed Ahmed Mahmoud, ya ce akwai yiwuwar a cikin mako mai zuwa su gurfanar da hambararren shugaban kasar Omar Hassan Al-Bashir a gaban kotu, domin amsa tuhume-tuhumen da ake yi masa ciki har da taimaka wa ayyukan ta’addanci baya ga kisan kare-dangi.

Alwaleed Sayed ya shaida wa manema labarai a birnin Khartoum cewa, baya ga Al-Bashir, akwai manyan jami’an gwamnati akalla 41 da za su fara fuskantar shari’a akan laifuffuka masu alaka da cin hanci da rashawa.

Kalaman na Alwaleed dai su na zuwa ne, a daidai lokacin da gwamnatin soji ta kasar Sudan ta dakatar da shirin ta na tabbatar da wata doka da za ta bada damar karbe wasu muhimman wurare daga hannun dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya da ke aiki a yankin Afrika, ciki har da helkwatar su.

Leave a Reply