Home Labaru Habaka Tattalin Arziki: Sarkin Bichi Ya Sha Alwashin Sauya Rayuwar Al’Ummar Masarautar...

Habaka Tattalin Arziki: Sarkin Bichi Ya Sha Alwashin Sauya Rayuwar Al’Ummar Masarautar Sa

68
0

Masarautar Bichi ta fara tattaunawa da masu zuba jari domin samar da wani katafaren wuri da zai rika samar da wuta mai amfani da hasken rana.

Sarkin Bichi mai martaba Alhaji Nasir Ado Bayero ne ya fadawa BBC hakan a wata tattaunawa ta musamman albarkacin bikin ba shi sanda da za a yi ranar Asabar din nan.

Sarkin ya kara da cewa masarautar sa na shirin inganta babbar kasuwar hatsi ta Najeriya da ke Dawanau.

Sarkin ya ce wannan mataki ne da zai inganta rayuwar al’ummar masarautar sa musamman yankunan karkara.