Home Labaru Kiwon Lafiya Yajin Aiki: Kotu Ta Umarci Likitoci Su Koma Bakin Aiki

Yajin Aiki: Kotu Ta Umarci Likitoci Su Koma Bakin Aiki

44
0
Nigerian Doctors Vow To Continue Strike
Nigerian Doctors Vow To Continue Strike

Kotun ma’aikata ta kasa da ke zama a Abuja ta umarci kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta dakatar da yajin aikin da ta ke yi.

Alkalin kotun John Targema ne ya bada umarnin, yayin da ya ke yanke hukunci a kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar.

Likitocin dai sun shiga yajin aikin ne a kan rashin biyan su albashi yadda ya kamata da sauran wasu dalilai.

Alkalin kotun ya ce, bayan duba da kuma nazari a kan rantsuwa da bukatar gaugawa da masu shigar kara su ka gabatar, Kotu ta yi biyayya ga dokoki kamar yadda aka gabatar mata, don haka ya bada umarnin cewa a dakatar da yajin aikin.