Home Labaru Cire Tallafin Man Fetur: Kungiyar Kwadago Ta NLC Ta Ba Gwamnatin Tarayya...

Cire Tallafin Man Fetur: Kungiyar Kwadago Ta NLC Ta Ba Gwamnatin Tarayya Shawara

238
0

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta ta ja kunnen gwamnatin tarayya ta guje daukar shawarar da Asusun bayar da lamuni na Duniya wato IMF ya bata na cire tallafin man fetur.

Kungiyar ta ce idan gwamnati ta biyewa wannan shawara, za a sami karin farashin man fetur, wanda a karshen mutanen Najeriya za su shiga cikin wani mawuyacin hali.

Shugaban kungiyar ta kasa Ayuba Wabba ya bayyana haka a  wajen wani taro na musamman da kungiyar kwadagon ta shirya a Abuja.

Ayuba Wabba, ya  ce a duk lokacin da Asusun IMF ya yi magana akan Najeriya, babu abinda ya ke kira sai a cire tallafin fetur, a kara nakasa darajar Naira, da kuma yunkurin kawo yadda za a kashe kasuwancin  Najeriya.

Wabba, ya soki tsarin da ake bi wajen biyan tallafin fetur a yanzu,  inda ya yi kira ga gwamnati  ta gyara matatun mai.

 Asusun IMF na ganin cire tallafin man fetur zai kara bunkasa tattalin arzikin kasa.

Leave a Reply