RSF ta ce za ta bude hanyoyin fita daga yankin El-Fasher,
sakamakon fadan da ya sake rincabewa a makwannin nan.
rundunar ta wallafa a shafinta na X , ta ce za ta taimaka wa jama’a su bar yankin zuwa wasu sassan kasar tare da ba su kariya.
RSF ta bukaci mazauna El-Fasher su kaurace wa yankunan da ake fada da ma inda za su iya kai wa farmaki.
Fiye da shekara guda kenan da Sudan ta fada cikin rikicin shugabanci
tsakanin shugaban rundur sojin kasar, Abdel Fattah al-Burhan da kuma na RSF da ke karkashin jagorancin Mohamed Hamdan Daglo.
Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutum fiye da 15,000 a cewar kwararru a Majalisar Dinkin Duniya.