Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce sami nasarar hallaka ‘yan fashi da makami 9 a dajin Akilbi kusa da hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar DCP Frank Mba, ya ce hukumar ta yi galaba akan masu ta’ada ya yin wata misayar wuta a tsakanin su.
Mba, ya ce hukumar ta sami nasarar cafke wasu miyagun makamai da suka hada da bindigogi daban-daban tare da kwanson alburusai da kuma harsashai.
Ya ce jami’in dan sanda guda ya raunata inda a halin yanzu ya ke jinya a asibiti.
DCP Frank Mba, ya ce mukaddashin shugaban rundunar ‘yan sanda Muhammadu Adamu, ya bayyana gamsuwa dangane da kwazo da kuma nasarori da hukumar ‘yan sandan ta samu musamman a yayin ci gaba da yakar ta’adanci da kuma garkuwa da mutane da sauran laifuka.