Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya wato EFCC, ta yi nasarar karbe wasu kadarorin tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke.
Ofishin hukumar EFCC dake jihar Legas ne ta sami nasarar karbe wasu dukiyoyi na Diezani Alison da kuma wani mutum mai suna Donald Chidi Amangbo.
Daga cikin kadarorin da hukumar ta sa aka karbe akwai wani makeken gida dake titin Nnmadi Azikiwe a Fatakwal na jihar Ribas.
Mai shari’a na babbar kotun tarayya da ke Legas Chuka Obiozor ya bada damar karbe wadannan dukiyoyi na minister, sannan kuma ya mika ga gwamnati.
Mai shari’a Chuka Obiozor ya bada damar hukumar EFCC ta rike kadarorin kafin a kammala binciken da za ayi.
You must log in to post a comment.