Home Labarai EFCC Ta  Ƙaddamar Da Gidan Rediyo

EFCC Ta  Ƙaddamar Da Gidan Rediyo

330
0
images 2024 02 22T201133.166
images 2024 02 22T201133.166

Gwamnatin Tarayya da Hukumar Yaƙi Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa,

EFCC, sun sha alwashin daƙile yaɗuwar labaran ƙarya a Najeriya.

Ministan Yaɗa Labarai , Mohammed Idris da shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ne suka bayar da wannan tabbacin,

yayin da suke ƙaddamar da gidan rediyon EFCC da ke kan mita 97.3 a zangon FM a Abuja a hukumance.

Muhammad Idris ya ce kamata ya yi a yaba wa hukumar kan yadda take yaƙi da cin hanci da rashawa .

Ministan ya ƙara da cewa babu wani ɗan Najeriya a yau da zai yi watsi da tasirin da EFCC ke yi.

Ya yaba da shirin gidan Rediyo da hukumar ta yi, inda yace za a ba ta cikakken ikon daƙile yaɗuwar jita-jita

Ya kuma bai wa hukumar tabbacin samun ƙarin goyon baya a ayyukan gidan rediyo da sauran ayyukan hukumar.

Leave a Reply