Home Labaru Buhari Ya Kalubalanci Manyan Hafsoshin Soji Su Kirkiro Sabbin Dabaru

Buhari Ya Kalubalanci Manyan Hafsoshin Soji Su Kirkiro Sabbin Dabaru

564
0
Buhari Ya Kalubalanci Manyan Hafsoshin Soji Su Kirkiro Sabbin Dabaru
Buhari Ya Kalubalanci Manyan Hafsoshin Soji Su Kirkiro Sabbin Dabaru

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci manyan hafsoshin tsaron Nijeriya su gudanar da cikakken nazari game da tsare-tsare da dabarun da su ke amfani da su a yaki da ‘yan ta’addan kungiyar ISWAP, domin duba yiwuwar kirkiro sabbin dabaru.

Buhari ya bada umurnin ne, yayin taron kara wa juna sani a kan harkar tsaro karo na 10 da tsofaffin daliban kwalejin tsaro ta kasa su ka shirya a Abuja.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan tsaro Bashir Magashi, ya ce sabbin hare-haren ta’addanci da ake samu su na faruwa ne sakamakon shan kayen da kungiyar ISIS ta yi a duniya, amma ya ce an ba hukumomin tsaro damar su shawo kan duk wani nau’i na ta’addanci a Nijeriya.

Ya samuwar burbushin ISIS a yankin Afirka ta yamma babbar barazana ce, shi ya sa ake hada kai da sauran kasashen Afirka da kungiyoyin kasa da kasa domin takaita wanzuwar ta’addancin tare da karya lagon ‘yan ta’addan.

Buhari ya kara da cewa, babu shakka Sojojin Nijeriya sun ci galaba a kan mayakan Boko Haram, kuma akwai bukatar su sake duba tsare-tsaren don samun galaba a kan mayakan ISWAP da ke kai hare-hare a sassan kasar nan.

Leave a Reply