Home Labaru Adamawa: Gwamna Fintiri Ya Yi Wa Ma’aikata 5,000 ‘Korar-Kare’

Adamawa: Gwamna Fintiri Ya Yi Wa Ma’aikata 5,000 ‘Korar-Kare’

563
0
Adamawa: Gwamna Fintiri Ya Yi Wa Ma’aikata 5,000 ‘Korar-Kare’
Adamawa: Gwamna Fintiri Ya Yi Wa Ma’aikata 5,000 ‘Korar-Kare’

Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, ya kori ma’aikata 5,000 ba tare da biyan su ladar zafin zaman rashin aikin yi ba.

Majalisar Zartarwar Jihar ce ta kafa kwamitin da ya bi diddigin ma’aikatan da gwamnatin baya ta jam’iyyar APC ta dauka aiki, inda ya gano an dauki ma’aikata sama da 5,000 ba bisa ka’idar daukar ma’aikata da gwamnatin Jihar Adamawa ta shimfida ba.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Adamawa Umar Pella ne ya yi wannan sanarwa a Gidan Gwamnatin jihar da ke Yola, inda ya ce duk ma’aikacin da ya san an yi ma shi daukar kwasan-karan-mahaukaciya tsakanin watannin Satumba da Mayu na shekara ta 2018  an sauke shi daga aiki kai-tsaye.

Sai dai Kwamishinan ya ce, mutum ya na da damar sake cika fom don sake duba daukar sa idan har ya cancanta.

Korar dai ta shafi dukkan wasu masu mukaman siyasa da gwamnatin jam’iyyar APC ta kafa a zamanin tsohon gwamna jihar Bindow.

Ya ce duk wanda aka ba mukamin siyasa a waccan gwamnatin, daga ranar 29 Ga watan Mayu babu ruwan wannan gwamnatin da shi.