Home Labarai APC Za Ta Zabi Shugaban Ta Cikin Wasu Jiga-Jigan Mambobin Ta 4...

APC Za Ta Zabi Shugaban Ta Cikin Wasu Jiga-Jigan Mambobin Ta 4 a Watan Fabrairu

93
0

Gabanin babban taron jam’iyyar APC da za a gudanar ranar 26 ga watan Fabrairu, an rage adadin masu neman shugabancin jam’iyyar, ciki kuwa har da gwamnoni da wadanda ke fadar shugaban kasa.

Wata majiya ce, shugaba Buhari da wasu gwamnonin sun
karkatar da akalar shugabancin jam’iyyar ga ‘yan takara hudu,
wadanda su ka hada da Tanko Al-Makura da Sanata Abdullahi
Adamu da Saliu Mustapha da kuma Abubakar Bawa Bwari
domin zabar shugaban jam’iyyar na kasa.

Majiyoyi daga sun ce, wani sashe na fadar shugaban kasa na
kallon su a matsayin wadanda za su maye gurbin gwamnan jihar
Yobe kuma shugaban riko na jam’iyyar Mai Mala Buni.

Duk da cewa wata majiya ta ce akwai matukar wahala a gane
ra’ayin shugaba Buhari a kan wanda ya ke goyon baya, amma
ana tsammanin yanayin shi ya nuna cewa ya fi bada fifiko ga
Tanko Al-Makura.

Sai dai masu adawa da Tanko Al-Makura sun ja hankalin masu
tallata shi da cewa, hukumar EFCC ta na kan gudanar da bincike
a kan sa.