Home Labarai Gwamnatin Kano Da Yan Adaidaita Sahu Sun Cimma Matsaya a Kan Kudin...

Gwamnatin Kano Da Yan Adaidaita Sahu Sun Cimma Matsaya a Kan Kudin Rajista

112
0

Matukan Keke NAPEP da gwamnatin Jihar Kano sun cimma
matsaya, game da ce-ce-ku-cen da ya kunno kai a kan karin kudin sabunta rijistar lambar Babura, lamarin da ya kai ga matukan sun gudanar da yajin aikin kwanaki uku.

A ranar Larabar da ta gabata ne, bangarorin biyu su ka cimma
matsayar bayan shafe tsawon sa’o’i 6 ana tattaunawa domin
lalubo bakin zaren lamarin.

Taron dai ya samu halartar lauyoyin kungiyar Adaidaita sahu, da
wakilin hukumar kula da zirga-zigar ababen hawa ta jihar ta
Kano KAROTA.

Matsayar da aka cimmawa ta haifar da da mai ido, inda aka rage
kudin sabunta rijistar daga Naira dubu takwas zuwa Naira dubu
5, yayin da kudin sabuwar rajista su ka koma Naira dubu 12
sabanin Naira dubu 18 da aka bayyana tun farko.

A bisa wani abu mai kama da gargadi dai, shugaban hukumar
KAROTA Baffa Babba Dan Agundi, ya ce duk wanda ya gaza
biyan kudin sabunta rijistar kan lokaci zai biya naira dubu 18 da
aka kayyade da farko, sai kuma naira dubu 8 ga duk mai bukatar
sabunta rijistar.

Leave a Reply