Home Home Kaddamar Da Ayyuka: Shugaba Buhari Ya Ce El-Rufa’i Ya Sa Ya Kasa...

Kaddamar Da Ayyuka: Shugaba Buhari Ya Ce El-Rufa’i Ya Sa Ya Kasa Gane Hanyar Zuwa Gidan Shi A Kaduna

88
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ayyukan cigaban da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa'i ya yi sun sa ya kasa kai kan shi gida duk da shekarun da ya yi a matsayin mazaunin Kaduna kafin zama shugaban Kasa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ayyukan cigaban da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa’i ya yi sun sa ya kasa kai kan shi gida duk da shekarun da ya yi a matsayin mazaunin Kaduna kafin zama shugaban Kasa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda ya kaddamar da ayyukan hanyoyi da gadoji da sauran ayyukan more rayuwa a yankin Kafanchan dake kudancin jihar Kaduna da kuma wasu ayyukan a kwaryar cikin garin Kaduna, ya ce Kaduna ta canza fasali karkashin gwamna Nasuru Ahmed El-rufa’i.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da hanyoyin da gwamna El-Rufa’i ya gyara, Shugaba Buhari ya ce Kaduna gida ce a gurin shi amma yanzu da kyar ne ya gane gidan shi sabili da yadda hanyoyin suka sauya fasalin birnin Kaduna.

Sai dai tuni Jam’iyyar PDP mai adawa a jihar Kaduna ta yi marhaban da zuwan shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kaduna, amma ta ce ziyarar siyasa ce tsantsa kuma ta kalubalanci gwamna El-rufa’i ya wuce yankin Birnin Gwari da Giwa don jajantawa mutanen da ke fama da hare-haren ‘yan-bindiga a yankin.