Home Labaru 2023: Sarakunan Jihar Legas Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Bola Tinubu

2023: Sarakunan Jihar Legas Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Bola Tinubu

236
0

Masu rike da sarautar gargajiya a Legas sun yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mubaya’a a zaben shugaban kasa mai zuwa na 2023.

Sarakunan sun bayyana goyon bayansu a karkashin jagorancin Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, a wani taro da aka shirya a Eko Hotels na Victoria Island.

A wannan taro da aka yi an tattauna akan matsayin masu sarautar gargajiya wajen kawo zaman lafiya da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ya ce sarakunan sun nuna suna tare da jigon jam’iyyar APC mai mulki, za su mara masa baya ya zama shugaban kasa bayan Muhammadu Buhari.

Leave a Reply