Home Labaru Rikicin Jos: An Tsananta Tsaro A Farfajiyar Majalisar Jihar Filato

Rikicin Jos: An Tsananta Tsaro A Farfajiyar Majalisar Jihar Filato

53
0

Magatakardan majalisar dokokin jihar Plateau Ponven Wuyep,  ya tabbatar da cewa an kara yawan jami’an tsaro  a farfajiyar majalisar amma ana ci gaba da aiwatar da sha’anonin mulki.

Sai dai ya  musanta rade-radin da ke yawo na cewa an garkame majalisar jihar baki daya, ya ce ba a rufe majalisar ba, saboda ana ci gaba da ayyuka kamar ko yaushe.

A ranar Asabar, a yayin taron manema labarai, majalisar ta bukaci jama’ar jihar su ba kan su kariya bayan rikicin da ke aukuwa a jihar a cikin kwanakin nan.

A wani harin tsakar dare da aka kai Yelwan Zangam a ranar Talata da ta gabata, an rasa rayukan mutum 37.

Wannan mummunan lamarin ya auku ne bayan mako daya da miyagu suka tare fasinjoji 27 suka kashe su a yayin da suke kan hanya inda suka ratsa ta Jos.