Home Labaru Majalisar Dattawa Ta Amince Da Naɗin Manyan Hafsoshin Sojin Nijeriya

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Naɗin Manyan Hafsoshin Sojin Nijeriya

71
0

Majalisar Dattawa ta amince da naɗin da shugaban ƙasa Bola
Ahmed Tinubu ya yi wa manyan hafsoshin sojin Nijeriya,
biyo bayan tantance su da aka yi a zauren majalisar.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya ce a lokacin tantancewar da aka yi a asirce, hafsoshin sojin sun amsa tambayoyi a kan lamurran da su ka shafi tsaro da kuma halin da Nijeriya ke ciki.

A ranar Litinin da ta gabata ne, Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar wata takarda, ya na buƙatar amincewar ta a kan naɗin da ya yi wa manyan hafsoshin.

Manyan hafsoshin da aka amince da naɗin su dai sun hada da Manjo-Janar C.G Musa a matsayin Hafsan hafsoshin dakarun Nijeriya, da Manjo-Janar T.A Lagbaja a matsayin Babban hafsan mayaƙan ƙasa, da Rear Admiral E.A Ogalla a matsayin Babban hafsan mayaƙan ruwa.

Sauran sun hada da AVM H.B Abubakar a matsayin Babban hafsan mayaƙan sama, da IGP Kayode Agbetokun Mai riƙon muƙamin shugaban ‘yan sandan Nijeriya, da Manjo-Janar EPA Unidianye a matsayin Shugaban Hukumar Tattara bayanan sirri ta kasa.

Leave a Reply