Home Labaru ‘Yan Majalisar Dokokin Nijeriya Sun Bukaci Karin Albashi

‘Yan Majalisar Dokokin Nijeriya Sun Bukaci Karin Albashi

40
0

‘Yan majalisar wakilai na neman a sake duba albashin su da
alawus-alawus da ake biyansu, biyo bayan cire tallafin man
fetur da halin da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki a halin yanzu.

Bukatar hakan dai ta na zuwa ne, bayan wani zama da ‘yan majalisar su ka yi, inda su ka bukaci shugaban majalisar Tajudeen Abass ya yi masu karin haske a kan dalilin da ya sa aka jinkirta biyan su albashi da alawus-alawus na watan Yuni.

Daya daga cikin ‘yan majalisar da ya bukaci a sakaya sunan sa saboda ba a ba shi damar yin magana a kan zaman majalisar zartarwa ba, ya ce sun yi maganar karin albashi ne kawai banda batun jinkirin biyan su.

Dan majalisar ya ce, sun sanar da shugaban majalisar cewa kudaden da ake biyan su a yanzu ba za su isa biyan bukatun su ba.

Sai dai shugaban majalisar a yanzu bai yi masu alkawarin samun karin albashi ko alawus-alawus ba, saboda a cewar sa lamarin ya na bukatar gyara a cikin kasafin kudi.

Leave a Reply