Home Labarai Lead British International School: An Rufe Makarantar Da Ɗalibai Suka Ci Zalin Wata...

Lead British International School: An Rufe Makarantar Da Ɗalibai Suka Ci Zalin Wata Yarinya A Abuja

37
0
lsb1 1216 579cf7eede493
lsb1 1216 579cf7eede493

Hukumomin wata makarantar sakandare mai zaman kanta a
Abuja babban birnin Nijeriya, Lead British International
School sun sanar da rufe ta har na tsawon kwana uku,
sakamakon rikicin da ya tayar da ƙura na “cin zalin wata
yarinya da wasu ɗalibai suka yi.”


Wannan na zuwa ne bayan da wani bidiyo da aka nuna ɗaliban na cin zalin yarinyar, wadda ita ma ɗaliba ce ta hanyar dukanta ya karaɗe shafukan sada zumunta, tare da jawo Allah- wadai da kiraye-kirayen neman hukumar makarantar ta ɗauki mataki.

A sanarwar da hukumomin makarantar suka yi a wani bidiyo da aka yaɗa a soshiyal midiya, an ga wani jami’in makarantar yana cewa an rufe ta bayan Ma’aikatar Mata ta Nijeriya ta bayar da umarnin yin hakan.

Ita ma rundunar ƴan sandan Nijeriya ta aika da “ƙwararrun” dakarunta makarantar domin yin bincike kan yamutsin da yake faruwa, a cewar SP Josephine Adeh, mai magana da yawun rundunar reshen birnin Abuja. Tun da fari dai masu amfani da kafofin sada zumunta suka riƙa yaɗa wani bidiyo da aka ga ɗaliban makarantar ta Lead British suna cin zalin wata ɗaliba ta hanyar duka da marinta.

Leave a Reply