Gwamnatin Jihar Kogi ta nesanta Gwamnan jihar Usman Ododo da zargin da hukumar EFCC ke masa na tserewa da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, a lokacin da jami’an hukumar suka je gidan tsohon gwamnan da ke Abuja domin kama shi.
Kwamishinan yada labaran jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ne ya bayyana hakan yana mai cewa Gwamna Ododo mutum ne da ya tsaya kai da fata wajen bin doka da oda.
A hirar da aka yi da shi, Fanwo ya kara da cewa zargin da EFCC ke wa Gwamna Ododo ba shi da tushe balle makama domin gwamnan bai taimaka wa tsohon gwamna Yahaya Bello wajen tssrewa daga gidan sa ba.
Fanwo ya musanta zargin da EFCC ke wa Gwamna Ododo na hana hukumar kama Yahaya Bello, yana mai kafa hujja da hukuncin wata babbar kotu da ta hana hukumar musguna wa tsohon gwamnan.
Ya ce babu wanda Yahaya Bello ke guje wa, umarnin kotu ya kare masa ’yancin sa na dan Adam, sai ya soki hukumar yana mai kalubantar ta ko tana da tabbaci game da ainihin inda Yahaya Bello yake.