Home Home Gwamnatin Najeriya Ta Haramta Ayyukan Kamfanin Crypto Na Binance

Gwamnatin Najeriya Ta Haramta Ayyukan Kamfanin Crypto Na Binance

47
0

Hukumar hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya, ta haramta ayyukan kamfanin hada-hadar kuɗaɗen Yanar Gizo  na Binace.

Matakin dai, ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin ta na yanar gizo, inda ta ce kamfanin Binance bai yi rajista da ita ba, don haka ne ta ce ta haramta ayyukan kamfanin a fadin Nijeriya.   

Sanarwar ta kuma gargaɗi ‘yan Nijeriya da ke mu’alama da kamfanin su dakata, idan ba haka ba duk abin da ya same su su kuka da kan su.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, an nusar da hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya game da shafin yanar gizo da kamfanin ke gudanarwa, inda ya ke neman ‘yan Nijeriya su zuba jari a harkar hada-hadar kuɗin intanet na cyrpto a shafin sa da wasu manhajojin wayar hannu.

Hukumar dai ta shawarci ‘yan Nijeriya su guji zuba jari a harkar hada-hadar kuɗaɗen intanet ta crypto a kamfanonin da ba su da rajista da ita.

Leave a Reply