Gwamnatin jihar Filato, ta bukaci hukumomin da ke da
hurumin kamo wadanda ke da hannu a kashe-kashen da aka yi
a karamar hukumar Mangu da kewaye su bayyana wadanda su
ka kama don a hukunta su.
Gwamnan Lalong ya kuma yi alkwarin tallafa wa dubban jama’ar da ke gudun hijira sakamakon rikicin.
Matasa da mata daga sassa daban-daban na jihar Filato dai sun taru wuri guda, domin nuna alhinin su a kan kashe-kashen da kuma bayyana bukatar gwamnati ta kawo karshen hare-haren da ake kai wa mutane.
Sama da Mutane 100 ne bayanai ke nuna cewa sun hallaka a hare-hare da aka kai karamar hukumar Mangu, yayin da dabbobi da dama su ka salwanta, sannan gidaje masu tarin yawa da wuraren ibada an kona su.
You must log in to post a comment.